ADDU'AR YAYE BAƘIN CIKI DA DAMUWA
Manzon Allah(SAW) ya ce: “Babu wani da wata damuwa ko baƙin ciki zai sameshi sai ya ce:
"اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ نَاصِيَتِي بِيَدِكَ مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي وَنُورَ صَدْرِي وَجلَاءَ حُزْنِي وَذَهَابَ هَمِّي".
“Allahumma innii abduka, wabnu abdika wabnu amatika, naasiyati biyadik, maadin fiyya hukmuk, adlun fiyya ƙadaa’uk, as’aluka bikullismin huwa laka sammaita bihi nafsak, au anzaltahu fii kitaabik, au allamtahu ahadan min khalƙik, auwista’tharta bihi fiy ilmil ghaibi indak, an taj’alal Ƙur’aana rabee’a ƙalbiy, wa nuura sadriy, wa jalaa’a huznii, wa zahaaba hammiy”.
Face Allah ya tafiyar masa da damuwansa da baƙin cikinsa, kuma ya canza masa shi da kwaranyewarsa.
(سلسلة الأحاديث الصحيحة 198)
A ƙarshe Manzon Allah(SAW) ya ce: ya kamata duk wanda ya ji su to ya koyesu.
FASSARA:
Yaa Allah, Ni bawanKa ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka, makwarkwadata a hannunka take, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma ƙaddararka a gare ni mai adalci ce, Ina rokonka da dukkan sunanKa, wanda Ka ambaci Kan ka dashi, ko Ka saukar dashi a cikin LittafinKa, ko Ka sanar da shi ga wani daga cikin halittunKa, ko Ka keɓance Kanka da saninsa a cikin ilimin gaibu da ke wurin Ka, da Ka sanya Al-Ƙur’ani ya zamto kaka ga zuciyata(kamar yanda ruwa yake raya kasa a lokacin damina), da haske ga ƙirjina, da yayewa ga baƙin cikina, da tafiyar da damuwata”.

Comments
Post a Comment