Posts

ADDU'OI INGANTATTU//01

Image
 ADDU'OI INGANTATTU//01 ADDU'AN BUDE SALLAH(A) سُبْـحانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْـدِكَ وَتَبارَكَ اسْمُـكَ وَتَعَـالَى جَـدُّكَ وَلا إِلهَ غَيْرُكَ. 💧"Subhanakallahumma wabihamdika, watabaarakas-muka, wata'aalaa jadduka, walaa ilaha gairuka". 💧"Tsarki ya tabbata gareKa Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun Sunanka sun yawaita, Mulkinka da girmanka sun daukaka, kuma babu abin bautawa da gaskiya wanda ba Kai ba". 

IDAN ALLAH YA BA KA DAMAN TAIMAKON 'DAN UWANKA TO KAR KA YI QASA A GUIWA

Image
 IDAN ALLAH YA BA KA DAMAN TAIMAKON 'DAN UWANKA TO KAR KA YI QASA A GUIWA Manzon Allah SAW yace: "Wanda duk ya kautar wa mumini wani baqin ciki daga cikin baqin cikin duniya, Allah zai kautar masa da wani baqin ciki daga baqin cikin Alqiyama. Wanda duk ya kawo sauqi ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauqi a duniya da lahira. Wanda ya suturce musulmi, Allah zai suturceshi a duniya da lahira. Lallai Allah yana taimakon bawa matuqar bawan yana taimakon d'an uwansa..." Muslim #Zaurandalibanilimi https://t.me/Zaurandalibanilimi

INA WANDA YAKE CIKIN DAMUWA DA KUNCI? INA ME NAMEN WATA BIYAN BUQATA?

Image
INA WANDA YAKE CIKIN DAMUWA DA KUNCI? INA ME NAMEN WATA BIYAN BUQATA? Matso kusa, Albishirinka... Manzon Allah (SAW) yace: "Wanda ya farka cikin dare, sai ya ce: "LAA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LAA SHAREEKA LAHU, LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU, WA HUWA ALAA KULLI SHAY'IN QADEER, ALHAMDULILLAH, WA SUBHANALLAH, WA LAA ILAHA ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR, WA LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH" , Sa'annan yace: "Yaa Allah ka gafarta mini ko ya yi wata addu'a, ZA A AMSA masa, idan kuma ya yi alwala ya yi sallah an karba sallarsa".  Imamul Bukhary ya ruwaito

ADDU'AR YAYE BAƘIN CIKI DA DAMUWA

Image
  ADDU'AR YAYE BAƘIN CIKI DA DAMUWA Manzon Allah(SAW) ya ce: “Babu wani da wata damuwa ko baƙin ciki zai sameshi sai ya ce: "اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ نَاصِيَتِي بِيَدِكَ مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي وَنُورَ صَدْرِي وَجلَاءَ حُزْنِي وَذَهَابَ هَمِّي". “Allahumma innii abduka, wabnu abdika wabnu amatika, naasiyati biyadik, maadin fiyya hukmuk, adlun fiyya ƙadaa’uk, as’aluka bikullismin huwa laka sammaita bihi nafsak, au anzaltahu fii kitaabik, au allamtahu ahadan min khalƙik, auwista’tharta bihi fiy ilmil ghaibi indak, an taj’alal Ƙur’aana rabee’a ƙalbiy, wa nuura sadriy, wa jalaa’a huznii, wa zahaaba hammiy”. Face Allah ya tafiyar masa da damuwansa da baƙin cikinsa, kuma ya canza masa shi da kwaranyew...